Gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa ta bada kasonta na Naira miliyan 15 domin aiwatar da shirin Babban Bankin Duniya rukuni na biyu na yaki da cutar kanjamau a jihar.
Darektar cibiyar yaki da cutar kanjamau ta jihar Yobe (YOSACA) Hajiya Farida Mamudo ce bayyana haka a Damaturu babban birnin jihar. Bisa ga cewarta, an rarraba kayan gwajin kwayar cutar guda 300 da magungunan rage kaifin cutar da ga dakunan jinya 20 a jihar.
Farida ta bayyana cewa, adadin wadanda suke kamuwa da cutar a jihar ya ragu daga kashi 2.7% a shekara ta 2008 zuwa kashi 2.1% a shekara ta 2010, dalili ke nan inji ta, da yasa gwamnatin jihar ta kara kaimi wajen yaki da cutar.
Tace duka-duka gwamnatin jihar Yobe zata bada dala miliyan 75 yayinda Babban Bankin Duniya zai rika bada gudummuwar dala miliyan biyar cikin shekaru biyar.
Hajiya Farida tace jihar Yobe ce ta farko a shiyar da ta kaddar da rukuni na biyu na shirin da kuma bada kasonta sabili da irin yadda jihar ta dauki batun da muhimmanci. Ta kuma yi kira ga ma’aikatun da aikin ya shafa su bada hadin kai domin ganin nasarar shirin.