Gwamnatin Jihar Yobe Ta Sanar da Kubuto 'Yan Matan Da Aka Sace

Alhaji Ibrahim Geidam gwamnan jihar Yobe

Alhaji Ibrahim Geidam gwamnan jihar Yobe

'Yan matan da kungiyar Boko Haram ta sace daga makarantarsu dake Dapchi ranar Litinin sun samu kubuta kamar yadda gwamnatin jihar Yobe ta sanar kuma yanzu suna hannun sojoji.

A daren jiya gwamnatin jihar Yobe ta ba da sanarwar 'yanto 'yan matan makarantar kwana ta garin Dapchi da 'yan kungiyar Boko Haram suka yi garkuwa dasu ranar Litinin da ta gabata.

Sanarwar da take dauke da sa hannun mai ba gwamnan jihar shawara akan harkokin yada labarai, Alhaji Abdullahi Bego na nuni da cewa sojoji sun 'yanto 'yan matan daga hannun 'yan Boko Haram. Ya ce yanzu suna hannun jami'an sojojin Najeriya.

A cewar Alhaji Bego, gwamnan jihar ya jinjinawa sojojin kasar da suka kwato 'yan matan. Amma duk da ikirarin, sanarwar bata bayyana adadin wadanda aka ceto ba.

A wata sanarwar da Alhaji Bego ya sake fitar wa ya ce makarantar na da dalibai 226 ne amma hamsin ne ba'a samu kaiwa garesu ba. Yanzu, injishi an ceto duk daliban.

Muryar Amurka ta tambayi kwamishanan ilimin jihar Alhaji Muhammad Yamin wanda ya yi karin haske akan nasarar da aka samu. A cewarsa an samu yaran ne kusa da iyaka da jihar Borno yanzu kuma suna babban birnin jihar.

Akwai wasu rahotanni dake cewa sojojin sun samu kubutar da 'yan matan ne sanadiyar bacin da motar 'yan Boko Haram din ta yi a tsakanin kan iyakar Borno da Yobe.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Yobe Ta Sanar da Kubuto 'Yan Matan Da Aka Sace - 2' 40"