Gwamnatin Jihar Taraba Ta Musanta Zargin Lakume Tallafin Naira miliyan 50 na Aliko Dangote

Alhaji Aliko Dangote

Gwamnatin jihar Taraba ta musanta cewa ta lakume kudaden tallafi na Naira miliyan 50 da hamshakin dan kasuwan nan Aliko Dangote ya bada domin a tallafawa wadanda rikicin yankin Mambila ya shafa

Wannan ne dai karon farko da gwamnan jihar Taraban, Arch.Darius Dickson Isiyaku ke maida martani game da bacewar Naira miliyan hamsin da dan kasuwan nn Aliko Dangote ya bada a matsayin gudummawa ga wadanda rikicin Mambilla ya shafa.

Ko a makon jiya sai da wasu shugabanin al’umman yankin Mambillan suka yi korafi na cewa fiye da watanni uku da bada gudummawar, har yanzu su basu ga koda kwandala ba.

To sai dai a martanin da ya maida, gwamnan jihar, ta bakin mataimakinsa Haruna Manu, yace kawo alkawari kawai Dangote yayi, domin babu ko anini da ya shigo aljihunsu,bare a raba.

To ko ya lamura suke yanzu a yankin? Barrister Bashir Muhammad Bape, dan majalisar dokokin jihar Taraba dake wakiltar mazabar Nguroje, ya bayyana cewa duk da hankula sun kwanta akwai bukatar kai tallafi.

Jihar Taraba jiha ta fuskanci rikice-rikice da sau tari ke da nasaba da kabilanci ko addini, lamarin da ya maida wasu yankuna kufayi, inda wasu ma ke ganin akwai sakaci a lamarin.

Ambassada,Hassan Jika Ardo, wanda shine jakadan Najeriya na yankin Caribbean na ganin akwai abun dubawa a lamarin.

Ga karin bayani a rahoton Ibrahim Abdulaziz

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Musanta Zargin Lakume Tallafin Nera miliyan 50 na Aliko Dangote - 3' 44"