Gwamnatin Jihar Taraba Ta Daga Darajar Masarautun Gargajiya

Nadin Sarauta a Jihar Taraba

Kafin dai wannan bukin bada sandar girman, wasu sun kai hari fadar sarkin Kwajji dake garin Puppule, domin nuna adawarsu da nada sabon sarkin da aka yi, Alh. Umar Buba Nyala,wanda ya gaji sarautar daga mahaifinsa da ya rasu kwanakin baya.

Da yake jawabi yayin bada sandar girman, gwamnan jihar Taraban Akitek Darius Dickson Isiyaku, yace gwamnatinsa zata cigaba da marawa sarakunan gargajiya baya, domin kwalliya ta biya kudin sabulu, don wanzar da zaman lafiya a jihar, jihar dai na faman farfadowa daga tashe tashen hankula.

Gwamnan ya mika sandar girmar ga sabon sarkin kwajji Umar Buba Nyal,a da aka daga darajar masarautar daga daraja ta uku zuwa ta biyu, da kuma wasu daggatai da suka koma darajar hakimai masu daraja ta uku.

Shi kuwa da yake jawabi a madadin sarakunan da aka daga darajar tasu sarkin Jen Alh. Ismaila Agwaru, ya tabbatar cewar zasu cigaba da bada nasu gudumawa wajen cigaban jihar.

Wannan ranar farin ciki ne a gare mu, kuma zamu bada namu gudumawa a matsayin sarakuna, iyayen kasa, domin samun zaman lafiya. Zamu yi aiki tukuru bada nuna son kai ga wani ko wasu ba, domin a samu cigaba a masarautun mu da jihar Taraba dama kasa baki daya.

Sarakunan da aka daga darajar tasu sun ko hada dana kwajjin Umar Buba Nyala, da Enoch Tanko Tabena sarkin Ndola, da na Tigun Ibrahim Etsu da kuma na Ichen Kurmi Ismaila Maiwuya.

Ga rahoton Ibrahim Abdul'aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Taraba Ta Daga Darajar Masarautun Gargajiya 2'40"