Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Sayo Motoci 98 Don Inganta Tsaro a Jihar

Motocin 'yan Sanda

Motocin guda casa'in da takwas gwamnatin jihar Sokoto tare da hadin gwiwar kananan hukumomi 23 da ke jihar ne suka sayo su domin taimakawa wajen kara samar da tsaro a jihar.

Wadannan motocin da aka sanya wa kayan sadarwa na zamani za a raba su ne ga jami'an tsaro domin taimaka musu a aikin da suke yi a fadin jihar kuma ana sa ran za su taimaka wajen kakkabe ayyukan ta'addanci musamman a yankin gabashin jihar da ke fama da hare-haren 'yan ta'adda.

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya ce ko bayan motocin gwamnati za ta samar da wata cibiya ta samar da bayanai masu muhimmanci da zasu taimaka wajen kara wanzar da tsaron rayukan jama'a.

Ana sa ran wannan yunkurin zai taimaka wa kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na yakar ‘yan ta'adda a gabashin jihar Sokoto.

Masana harkokin tsaro irinsu Auwal Bala Durumin Iya, kwararre a sha’anin aikata manyan laifuka da tsaro, ya ce hakan zai taimaka amma kafa wata hukuma da za ta kula da dazuzzuka, wadda za ta sa ido akan makiyaya, masu satar jama’a, ‘yan fashi da makami, masu safarar makamai, masu fasa kwabri da sauransu zai fi dacewa.

Bayan haka, ya na da muhimmanci a kafa wata cibiya ta musamman da za ta kula da harkokin tsaro musamman yin bincike da hasashen abinda ka iya faruwa don magance shi tun kafin ya faru, wannan shi zai taimaka wajen magance matsalar tsaro.

Saurari rahoton cikin sauti daga Muhammad Nasir.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Sokoto Ta Sawo Motoci 98 Don Inganta Tsaro a Jihar