Gwamnatin Jihar Sakkwato Ta Dakatar Da Hisba Yayin Binciken Fitar Da Tsiraicin Wata Yarinya

Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

Hukumar Hisbah a jihar Sokoto ta ce ta kammala bincike a kan hotunan tsiraici na wata yarinya da aka yada inda ake zargin wani dan babban jami'in gwamnatin jihar Sokoton, to amma kuma kwatsam sai gwamnati ta ba da sanarwar dakatar da ayyuukan hukumar.

Tuhumar da ake yi wa dan wani mai baiwa gwamnan jihar shawara na musamman da cin zarafin yarinyar ta hanyar yin lalata da ita da kuma daukar bidiyon tsiraicinta, ya fito fili ne bayan da mahaifiyar yarinyar ta kai koke a hukumar ta Hisbah ta jihar.

Matar ta ce bayan da wanda ake zargin ya yada hotunan a yanar gizo, dalilin da ya sa wanda ya yi niyyar aurenta ya ce fasa, alhali har an sa ranar auren na su.

Dr. Adamu Bello Kasarawa shi ne kwamandan hukumar Hisbah na jihar Sokoto, ya kuma shaidawa sashen Hausa cewa, matashin ya amsa cewa ya aikata abin da ake zarginsa da aikatawa. Ya ce binciken da aka gudanar a kan wadanda suka samu hoton bidiyo ya tabbatar da shine ya raba bidiyon ya kuma ce shi ya gama da yarinyar.

"Hukumar Hisbah ta zauna da iyayen yaran uku a kan wannan batu domin samun mafita amma iyayen yarinyar sun bukaci hukuma ta bi musu hakkin su kana a tabbatar da adalci a kan wannan cin zarafi," in ji kwamanda Kasarawa.

A karshen mako ne dai gwamnatin jihar Sakkwato ta fitar da wata sanarwa mai cewa ta dakatar da ayyukan Hisbah har sai kwamitin da ta kafa domin ya yi nasazari a kan dokar da ta kafa hukumar da kuma ayyukanta ya kamala aikin sa.

Matakin da gwamnati ta dauka na dakatar da ayyukan Hisba ya haifar da korafe-korafe da rubuce rubuce a kafofin sadarwa musamman Facebook cewa gwamnatin ta yi hakan ne saboda hukumar na bincike a kan aika-aikar da dan wani babban jami’inta ya yi.

Mai baiwa gwamna shawara na musamman a kan yada labarai, wanda kuma ya fitar da sanarwar ta karshen mako, Mohammed Bello, ya musunta cewa matakin na gwamnati na da nasaba da bincike da Hisba ke yi.

Ya ce "gwamna ya gano akwai matsaloli a hukumar ta Hisba, ya kuma gana da shugabannin hukumar ya tabbatar musu da cewa yana sane da matsalar dake cikin Hisbah kuma a kan haka ne ya kafa kwamitin."

Mai magana yawun iyalan Masur Bello Acida saurayin da fasa auren yarinyar, ya ce "tun da dai ba a riga an yi auren ba kuma saurayin ya ce ya janye don haka magana ta rage tsakanin wadancan dangi su daidaita tsakanin su."

Kungiyoyin fafatukar kare hakkin jama'a sun ce suna biye da batun don ganin anyi adalci.

Ga dai rahoton da Muhammad Nasir ya aiko mana daga Sakkwato:

Your browser doesn’t support HTML5

HISBAH TA KAMMALA BINCIKE A KAN BATURN FITAR DA TSIRAICI WATA YARINYA