A lokacin da ya ke amsa tambayoyin manema labarai a garin Muye, na yankin karamar hukumar Lapai, gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello, bai saki jiki ya yi wani dogon bayani ba akan lamarin, sai dai ya tabbatar da kamun tsohon gwamnan.
Ya ce, “Na karanta a jaridu dan haka ban san komi ba a kai, domon babu wani da ya gabatar mani da lamarin a hukumance” to amma daga bisani kwamishinan labarai na jihar Neja, Mr Jonathan Batsa, ya ce dama akwai korafe korafe da aka gabatar akan tsohon gwamnan.
Mr Jonathan, ya bayyana cewa akwai korafe korafe da dama da aka jingina a kan tsohon gwamnan wadanda a fili suke, amma tunda hukumar EFCC tana rike da shi, sai ta kammala binciken da ta ke yi, jama’a zasu ji cikakken lamarin da yayi dalilin cafke tsohon gwamnan.
Da aka nemi jin ta bakin sakataren yada labaran tsohon gwamnan ta wayar salula, Mr Israel Abije, ya bayyana cewa sai a ranar Juma’ar nan suke sa ran fitar da wata sanarwa a kan lamarin.
Mustapha Nasiru Batsari na da karin bayni.
Your browser doesn’t support HTML5