Baicin mummunan halin da asibitocin ke ciki ma'aikatan ma ba'a kula dasu kuma ba'a biyansu albashin da ya kamata gwamnati ta biyasu dalilin da ya sa likitoci da sauran ma'aikatan kiwon lafiya suna gujewa jihar.
Wani magidanci Malam Muhammad Sani wanda kwanan nan matarsa ta haihu ya shaidawa Muryar Amurka halin da ya shiga da asibitin gwamnati. Yace matarsa da tazo haihuwa an kaita asibitin gwamnati dake kusa da gidansa. Da isarsu asibitin aka rubuta masu magungunan da ya sayo da kkudi fiye da nera dubu biyu.
Basu yi anfani da magungunan ba kuma matarsa ko minti biyar bata yi ba ta haihu. Amma kafin a sallamesu sai da asibitin ya karbi nera dubu shida a matsayin kudin haihuwa.
Yanzu hatta ita kanta gwamnatin jihar ta tabbatar da tabarbarewa alamura a fannin kiwon lafiyar jihar. Dalili ke nan da gwamnatin ta kaddamar da dokar ta baci akan harkokin kiwon lafiya.
Kwamishanan labarai na jihar Jonathan Batsa yace mutane na wahala saboda yanayin asibitocin gwamnatin jihar. Yace a wasu asibitocin ma babu gadajen kwana, ba kayan aiki kana mutane suna wahala tare da mutuwa. Dalili ke nan da gwamnati ta kafa dokar.
Kwamishanan lafiya na jihar Dr Mustapha Jibril yace tsohuwar matsala ce da suka gada amma suna kokarin shawo kan al'amarin. Yace an yi fiye da shekaru goma ba'a dauki ma'aikatan kiwon lafiya ba duk da cewa mutane suna mutuwa kana kuma ba'a biyan ma'aikatan albashinsu na zahiri. Gwamnan jihar ya ga idan ba'a gyara lamura ba da wuya su cimma nasara.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5