A kokarinta na neman kawar da cutar shan inna gwamnatin jihar Neja ta kaddamar da shirin bada allurar rigakafin cututuka dake hallaka yara kanana wanda za'a share kwanaki takwas ana yi.
WASHINGTON, DC —
Daga jiya Talata har kwanaki takwas masu zuwa za'a cigaba da aikin bada allurar rigakafin cututuka dake hallaka yara a jihar Neja.
Za'a ba yara 'yan kasa da shekaru biyar allurar a cibiyoyin kiwon lafiya na musamman da aka kebe domin aikin. Ahmed Ndagi Muhammed daraktan sashen dake kula da cin abinci masu gina jiki na ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar yayi karin haske akan irin cututukan da za'a yi rigakafinsu.
Yace akwai allurar polio ko cutar shan inna da aka saba yi da wasu. Zasu bada maganin ciwon hanta da na tsutsotsin ciki. Za'a kuma ba yara wasu magunguna dake kara ma yara karfin jiki.
Dr Yabagi Aliyu darakta a matakin farko na ma'aikatar kiwon lafiya yace an tanadi ma'aikatan da zasu yi aikin duk cikin fadin jihar domin tabbatar da ba'a samu cikas ba.
Tuni shugabannin al'umma suka himmatu wajen bada goyon baya da wayar da kawunan al'ummominsu. Alhaji Abubakar Sadiq babban darakta ne a ma'aikatar kula da harkokin makiyaya yace sun kira taron mata sun fadakar dasu akan aikin bada allurar rigakafin. Sun wayar da kawunan mutane kuma kamar yadda yace sun fahimta.
Kwamishaniyar kiwon lafiya ta jihar Hajiya Hadiza Abdullahi ita ta wakilci gwamnan jihar a wurin kaddamar da aiin. Tace gwamnati tana fata kowa zai yi nasa ya bada hadin kai domin a cimma nasara. Ta kira iyaye mata da maza su yadda da su domin aikin na tabbatar da lafiyar 'ya'yansu ne.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5