Gwamnatin jihar Neja ta kammala bada horon sana’o’in dogaro da kai ga wasu yara ‘yan mata 39 ‘yan asalin jihar, wadanda gwamnatin jihar Kebbi ta mayar da su gida daga inda su ke Al’majiranci.
Mai martaba Sarkin Gwandu na jihar Kebbi Alh. Muhammadu Iliyasu Bashar ne yasa aka mayar da yaran ‘yan kasa da shekaru goma sha daya zuwa jihar su ta asali, aka kuma damka su a hannun iyayensu tun kimanin watanni biyu da suka wuce, al’amarin da yasa Gwamnatin jihar ta Neja ta dauki wannan mataki na koyar da su sana’o’in dogaro da kai.
Babban jami’in hukumar kula da kare hakkin yara a jihar Neja Suleman Makusidi da ya shugabanci aikin, ya ce bayan horodda da yaran kuma an basu tallafin kayan aikin duk abin da aka koyar dasu.
An koyar da ‘yan matan yadda ake yin Sabulun Wanka da Wanki, Man shafawa, da kuma yadda ake yin Taliyar hannu da Turare da dinki. Al’amarin da ya farantawa yaran da iyayensu rai kamar yadda wasu daga cikinsu suka bayyana wa wakilin muryar Amurka.
Wannan dai yana zuwa ne adaidai lokacin da Gwamnatin jihar Neja ke shirin karba ko mayar da dukkanin Almajirai zuwa garuruwan su na asalin, in ji Gwamnan jihar Abubakar Sani Bello.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5