Gwamnatin Jihar Neja Ta Gargadi Malaman Tafsiri

Musulmai na yin sallah

Gwamnatin Jihar Neja Ta Gargadi Malaman Tafsiri su guje ma yin wa'azin da zai ingiza mutane su shiga tayar da hankula
Gwamnatin Jihar Neja ta ce ta aika da takardun jan kunne ga duk malaman da ke tafsiri lokacin azumi da su guje ma yin wa'azin da zai tayar da hankulan mutane.

Gwamnatin ta ce ta dauki matakin ne ganin yadda yanayin tsaro yake a kasar. Ta na son malaman malaman su kauce wa kalamun da zasu harzuka jama'a. Su kuma kaucewa kalamun siyasa a tafsiransu.Kwamishanan kula da harkokin addinai a jihar ya ce sun raba takardun ma duk masarautu takwas dake fadin jihar. A cikin takardar da aka aika an umurci sarakuna su gayawa hakimansu su kuma fadawa malaman tafsiri lokacin azumi cewa ban da zage-zage ko kawo kalamun siyasa sabili da yanayin da kasar ke ciki. Ya ce idan babu zaman lafiya ba za'a samu daman yin ibada ba cikin walwala. Da aka tambayeshi ko akwai dokar da ta fayyace yadda malami zai yi wa'azi sai ya ce babu. To amma suna son duk masu wa'azi su yi koyi Annabi Mohammed (SAW)

Su ma malaman sun ce sun shirya yadda zasu yi tafsiri domin sun yi taro sun kuma cimma matsayi game da abubuwan da suka kamata su yi. Sun tattauna sun kuma duba yadda zasu gudanar da tafsiransu.

A wani mataki kuma domin taimakwa al'umma gwamnatin jihar ta kaddamar da shirin sayerwa mutane kayan abinci da na masarufi da rangwame kamar yadda gwamnan jihar Dr. Muazu Babangida Aliyu ya yi bayani.

Ga rahoton Mustafa Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Neja Ta Gargadi Malaman Tafsiri