Hukumar dake kula da cututtuka masu yaduwa ta gwamnatin tarayya ita ce tace an samu barkewar cutar sankarau a jihar ta Legas.
Dr Jide Idris a taron da yayi da manema labarai yace babu kanshin gaskiya a labarin barkewar cutar a jihar kuma kawo yanzu babu alamar cutar a jihar. Amma yace ko shakka babu an samu barkewar cututtuka dake da nasaba da cutar sankarau musamman a arewacin Najeriya. To saidai a jihar Legas babu wani rahoton bazuwar cutar musamman sankarau irin na C mai kisa nan da nan.
Dr Jide Idris yace akwai cutar sankarau iri biyu. Akwai mai zafin akwai kuma wadda bata da zafi. Yace akwai wadda bata da hatsari kuma ana samunta a wasu jihohi amma ba irin na arewacin Najeriya ba.
Dangane da matakan da gwamnatin jihar ke dauka domin hana bullar cutar a jihar, Dr Jide Idris yace akwai jami'an kiwon lafiya da suka saba fadakar da al'umma game da yadda zasu kula da lafiyarsu. Jami'an suna zagaya koina cikin duka kananan hukumomin jihar domin fadakar da al'umma su kasance cikin shiri da daukan matakan rigakafi.
Garahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5