Kone-konen da matasan suka yi ya sa gwamnatin jihar Kaduna dauke taronta na majalisar tsaro zuwa garin Kafanchan hedkwatar karamar hukumar Jama'a inda aka tattauna abubuwa da dama da suka jibanci tsaro.
Kafin su soma taron sai da gwamnan jihar da tawagarsa suka zagaye wuraren da aka kone a garin biyo bayan zang-zangar sannan ya kai ziyara fadar sarkin Jama'a.
A fadar sarkin gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai ya tabbatarwa jama'ar garin cewa gwamnati zata zakulo duk masu hannu a zanga zangar kana a hukumtasu ko su wanene ko menene ma addininsu. Saidai gwamnan ya roki jama'a su dinga ba mutane hakuri tare da gaya masu akwai hukuma kuma duk wanda aka yiwa ba daidai ba ya shaidawa hukuma domin a dauki mataki.
Sarkin Jama'a Alhaji Muhammad Isa Muhammad II yace zanga-zangar ce ta zunguro fitinar. Inji sarkin jami'in 'yansanda ne ya bada izinin a yi zanga zangar amma kuma ba'a wanye lafiya ba.
Kantoman karamar hukumar Dr Katuka yace babu wani rahoto a hukumance cewa wani ya rasa ransa baicin mutun daya da ya ji rauni.
An kafa dokar ta baci ta hana fita na sa'o'i ishirin da hudu lamarin da ya sa mutanen garin suna rokon Allah ya kawo masu sauki.
Duk da dokar hana yawo wasu mata sun fito suka yi zanga zanga tsirara.
Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5