Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sassauta Dokar Hana Fita A Kananan Hukumomi Biyu

Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El-Rufai.

Makonni biyu ke nan da rikici ya barke a garin Kafanchan dake karamar hukumar Jama'a lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta sa'o'i 24 a karamar hukumar tare da makwafciyarta Zangon Kataf da kuma Kaura

Yayinda gwamnatin ta sassauta dokar hana fita a kananan hukumomin Jama'a da Zangon Kataf ita ko karamar hukumar Kaura zata ciga da zama cikin dokar har sai wani lokaci.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Mr. Samuel Aruwan yace daga yanzu dokar hana fita a kananan hukumomin biyu zata fara aiki ne daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida safe kowace rana. Amma saboda dalilai na tsaro alummar karamar hukumar Kaura zasu cigaba da zama cikin gidajensu ba tare da fita zuwa koin aba har sai abun da hali yayi.

Rikicin da ya samo asali a Kafanchan shi ya yadu zuwa wasu kananan hukumomin dake makwaftaka da karamar hukumar Jama'a.

ASP Aliyu Usman mai magana da yawun rundunar 'yansandan jihar yace suna iyakacin kokarinsu domin su kawo karshen rikicin. Baicin kaddamar da binciken abun da ya faru a Kafanchan rundunar 'yansandan zata kafa sansanin 'yansandan kwantar da tarzoma a yankin.

Saidai wasu na ganin malaman addini da na siyasa suke ruruta wutar rikici a yankin kudancin Kadunan.

Ga rahoton Isa Lawal Ikara da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Sassauta Dokar Hana Fita A Kananan Hukumomi Biyu - 4' 33"