Gwamnatin Jihar Filato Na Shirin Maida Almajirai jihohinsu

Gwamnatin jihar Filato ta ce za ta maida daukacin almajiran dake jihar zuwa garuruwansu na asali.

Gwamnan jihar Simon Lalong ne ya bayyana hakan, ya kuma sassauta dokar killace jama’ar jihar daga yau Jumma’a zuwa ranar Lahadi don su samu damar fita sayen kayan abinci kafin a komawa dokar ranar Litinin.

Lalong ya ce gwamnati ta dauki matakin maida almajiran ne saboda barazanar cutar coronavirus.

Muhammadu Dahiru Alaramman wata tsangaya a Jos, ya ce kamata ya yi da gwamnati ta tuntubesu kafin daukar wannan matakin.

Wasu almajiran sun bayyana rashin jin dadinsu da matakin na maida su jihohinsu.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Jihar Filato Na Shirin Maida Almajiran Jihar jihohinsu