Shugaban ma'aikatan jihar shi ya shaidawa manema labarai hakan a birnin Maiduguri inda yace tuni ma gwamnatin ta kebe kudaden.
Gwamnan jihar ya bada izinin biyan kudaden kama daga na ma'aikatan jihar har da na kananan hukumomi. Yace sun shirya su soma biya domin kudaden suna nan.
Gwamnati ta kafa kwamitoci ukku da zasu tabbatar an biya kudaden. Barrister Yakubu Bukar yace duk da matsalar rashin tsaro da jihar ta fuskanta ko wata guda ba'a kasa biyan ma'aikata ba, kuma har yanzu zasu tabbatar an biya kowane ma'aikaci hakkinsa aduk lokacin da wata ya kare.
Acewar Barrister Yakubu Bukar gwamnatin jihar ta samo kudaden ne daga tallafin da gwamnatin tarayya ta bayar. Kwana kwanan nan aka samu wasu kudade daga Paris Club da gwamnatin tarayya ta rabawa jihohi.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5