Cibiyar kare yaduwar cututtuka ta Najeriya da ake kira NCDC a takaice, ta fitar da sanarwar bullar cutar ta shawarar a karamar hukumar Alkaleri, a jihar Bauchi bayan da aka tabbatar da cewa wani dan kasar waje da ya je jihar Kano bayan ya ziyarci dajin shakatawar Yankari dake jihar ya kamu da cutar.
Likita Rilwan Muhammed, shine shugaban hukumar ayyukan lafiya a matakin farko a jihar Bauchi, ya bayyana yadda cutar shawarar ta fara a jihar Bauchi da kuma alamomin cutar da suka hada da masassara, amai, ko fitar jini ta baki ko ta ido, ko ma a fitsari.
Tuni dai gwamnatin jihar Bauchi tare da gwamnatin tarayya da kuma tallafawar hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya suka kaddamar da aikin bada rigakafin cutar a fadin jihar da kuma yin feshi ta jirgin sama domin kashe sauron dake ya cutar.
A gefe guda kuma, hukumar lafiya ta duniya, a ta bakin jami’in ta, dakta Adamu Ibrahim Musa Ningi, ya shaida irin rawar da suka taka don kawar da sauron dake kawo cutar shawara.
Ga karin bayani a cikin sauti daga Abdulwahab Muhammed.
Your browser doesn’t support HTML5