A kokarin da Najeriya ke yi na yaki da cutar COVID-19, gwamnatin jihar Bauchi tare da hadin gwiwar kwamitin bunkasa shiyyar arewa maso gabas wato NEDC ta bude cibiyar gwaje-gwajen cututtuka a jihar, a daidai a lokacin da rahoto ke nuni da cewar shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 a jihar, kuma mataimakin gwamnan jihar, Senata Baba Tela ya kamu da cutar coronavirus.
An bude cibiyoyin gwaje-gwajen cututtuka guda asharin da tara (29), tare da tallafi daga kwamitin bunkasa shiyyar arewa maso gabas wato NEDC.
Farfesa Sani Malami shi ne ya jagoranci tawagar kwararru a fannin kimiyya da aikin samar da cibiyar, ya yi wa wakilin muryar Amurka Karin bayani kan aikin gina cibiyar, inda ya ce, cibiyar gwaje-gwajen ba za ta tsaya kan gwajin cutar coronavirus kadai ba ne, harda cutar Lassa, da dai sauransu.
Kwamishinan ayyukan lafiya na jihar Bauchi Dr. Aliyu Muhammed Maigoro ya ce, cibiyar gwaje-gwajen an samar mata kayan aikin da duk ya kamata kuma ake bukata wajen gwajin cututtuka.
Babban mai bada shawar ga gwamnan jihar Bauchi a fannin yada labarai, Alhaji Muktar Gidado ya tabbatar wa wakilin muryar Amurka cewa, shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus kuma mataimakin gwamnan jihar Senata Baba Tela ya kamu da cutar.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Abdulwahab Muhammad.
Your browser doesn’t support HTML5