Tuni ma aka dau kwararran matakan ko-ta-kwana a manyan asibitocin jihar Adamawan,don gudun abun da ka iya faruwa,inda ake gargadin jama’a da a kula.
Domin ko a shekaru biyu da suka shige an samu bullar cutar a Adamawa lamarin da ya janyo hasarar rayuka ciki ko harda wani likita, to ko wani hubbasa ne jamaar jihar suka yi?
Domin neman samun wannnan bayanin ne wakilin sashen Hausa IbrahimAbdul Azeez ya leka babban asibitin dake garin Yola, wadda it ace tayi fama da wadanda wannan zazzabin ta Lassa ta kama, Farfesa Muhammadu Awal babban Darektan asibitin yayi wa Ibrahim din bayanin matakan da suka dauka a halin yanzu.Ga kuma abinda yake cewa.
‘’Har zuwa yanzu dai ba wanda aka kawo mun kira likitocin dake kula da wannan cutar sun hadu sun duba idan ma akwai mara lafiya mai wannan cutar sun fadawa maaikatan dake sashen hadurra da kulawar gaggawa, inda masu wannan cutar ke far zuwa cewa ga alamomin, don haka idan sunga wani wani mai alama cutar sais u kebe shi akwai wajen kebewa da kuma kayan da likitoci zasu sa domin kare su daga kwasan cutar, amma zuwa yanzu ba wanda aka samu da wannan cutar’’.
Wannan dai yana zuwa dai-dai lokacin hukumomin kiwon lafiya dake makwabtaka da Adamawan ke jinyar wadanda suka kamu da zazzabin Lassan, inda rahotanni ke cewa adadin mutanen da suka mutu ya karu da mutum 5.
To sai dai kome ke kawo wannan cutar, ga kuma amsar da Dr Yunusa Wuza shine babban darektan cibiyar kiwon lafiya dake Jalingo wato FMC inda ake jinyar wasu game da zazzabin na lassa ga bayanin da yayi.
‘’Wannan cutar akwai wasu irin beraye da sukan kamu da wannan kwayoyin cutar berayen nan kuma idan suka shigo gidajen mutane ko kuma su hau kwanukan da ake sa abinci ko kuma inda aka ajiye abinci suka hau suka yi fitsari akai to muddin mutum yaci wannan abincin ko kuma yasa hannu inda wadannan berayen suka yi fitsari to mutum yana iya kamuwa da wannan cutar’’
Ga IbrahimAbdul Azeez da Karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5