Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da hukuncin kisa ga masu yiwa yara kasa da shekariu 10 fyade kamar yadda dokar kare yara ta tanada
Bisa doka, duk wanda aka samu da laifin yiwa yarinya ‘yar kasa da shekaru 10 fyade, za a yanke masa hukuncin kisa
Kwamishinan shari'a kuma Atoni Janar na jihar, Dakta Musa Adamu ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a karamar hukumar Dutse dake zama fadar gwamnatin jihar inda ya ce duk wanda aka samu da laifin zai fuskanci hukuncin ba tare da wani zabi ko mafita ba
A wata hira da aka yi da shi ta gidan talabiji na Channels, Dakta Musa ya bayyana cewa, idan za’a iya tunawa a farkon wannan shekarar ne gwamnan Jihar ta Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya sanya hannu kan dokar hana cin zarafi da ta’addanci wadda ta tanadi hukuncin kisa ga masu fyade tare da zabin daurin rai-da-rai, amma a kwanan nan gwamnati ta sanya hannu kan dokar kare hakkin yara wadda ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya yi wa yarinya ‘yar kasa da shekara 10 fyade.”
Ya ce jimillar shari’a 196 aka samu yayin da aka shirya shawarwarin shari'a 178 kan korafe-korafen da aka samu. A farkon shekarar nan, Gwamna Mohammed Badaru Abubakar ya rattaba hannu a kan dokar hana cin zarafi, wacce ta tanadi hukuncin kisa ga masu lalata da mata ta karfin tsiya amma da zabin daurin rai da rai.
Ya kara da cewa, a baya-bayan nan, gwamnati ta kuma sanya hannu a dokar kare kananan yara, da ta yanke hukuncin kisan kai ga duk wanda ya haike wa yarinya 'yar kasa da shekara 10. “A cikin jimillar shari’o’in, 90 sun kasance na fyade; 27 kisan gilla; luwadi yana da 31; garkuwa da mutane na da 18; lalata biyu; ayyuka na babban alfasha biyu; fashi da makami guda 20 yayin da laifuffukan karya dokar tuki ke da biyu.
Kwamishinan shari'ar ya kara da cewa, ma’aikatar ta gabatar da kara tare da kare jimillar kararraki 25 a gaban kotun daukaka kara, reshen Kano, sannan ta kuma kammala shari’ar laifuka 83 a gaban manyan kotuna takwas da ke Birnin Kudu, Dutse, Gumel Hadejia, Kazaure da Ringim.
Kwamishinan ya kuma koka da jinkirin shari’ar da ake samu a matsayin daya daga cikin manyan kalubalen da ma’aikatar ke fuskanta, wanda a cewarsa ba wai a jihar Jigawa ba ne, ya kuma kara da cewa za a iya rage matsalolin da ke da nasaba da jinkirin shari’ar laifuka ta hanyar amfani da fasahar zamani da ta dace.