Sai dai ‘yan gwagwarmayar shugabanci na gari sun bukaci hukumomin jihar da su guji amfani da hukumar wajen yakar abokan hamayyar siyasa.
Tuni dai kudirin dokar da za ta kafa wannan hukuma ya tsallake karatu na daya dana biyu a zauren majalisar dokokin jihar ta Jigawa.
Dr Musa Adamu Aliyu dake zaman kwamishinan shari’a kuma babban Atoni na jihar yace fassalin hukumar na kaman ceceniya da EFCC da ICPC, amma akwai sabbin al’amura.
Comrade Misbahu Basirka shine shugaban zauren, ya kuma ce da alama dai zauren gamayyar kungiyoyin fararen hula na Jigawa na maraba da wannan yunkuri na gwamnatin jihar dake samun tallafin ofishin majalisar dinkin duniya dake Najeriya.
Sai dai Barrister Amina Umar ta Ofishin lauyoyi masu bada tallafin shari’a wato legal Aid council dake Dutse tace akwai bukatar majalisar dokokin Jigawa ta samar da diraka ga wannan hukuma.
A baya dai an sha zargin masu rike da madafun iko a Najeriya da mayar da hukumomin yaki da rashawa karnukan farauta akan ‘yan hamayya.
Bayan majalisar dokokin jihar ta daidaita kundin dokar, ana sa ran gwamna Badaru Abubakar zai rattaba hannu cin hanzari domin hukumar yaki da rashawar ta Jigawa ta fara aiki gadan-gadan.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5