Gwamnatin Nijar Tace Sai Ta Gano Wadanda Suka Kashe Sojojinta Domin Daukar Fansa

  • Ladan Ayawa

Shugaba Muhammadu Isoufou na Niger

Kwanaki biyu bayan harin ‘yan taadda da ba a san ko su wanene ba suka abka wa jamiaan tsaro dake bada kariya ga sansanin ‘yan gudun hijira na Talzalit a cikin gundumar Tasara a cikin jihar Tahaou a cikin jamhuriyar Niger inda suka hallaka jami’an tsaro 22.

Ofishin ministan tsaron kasar ya fitar da wata sanarwa da kanar Mustapha kakakin ofishin ministan ya karanta a cikin daren jiya a gidan talabijin ta kasa.

Yayi Magana a cikin harshen faranci cewa yanzu haka an fatattaki wadanda suka aikata wannan danyen aikin wadanda suka arce zuwa kasar Mali domin a dakatar dasu domin yi musu hukuncin da ya dace su.

Sanarwan taci gaba da cewa wannan harin Niger ba zata yafe ba sai ta dauki fansa.

Kanar Mustafa yace yanzu haka an kebe kwanaki biyu na zaman makoki a duk fadin kasar ta Niger.

Ga Haruna Mammam Bako da Karin bayani 2’54

Your browser doesn’t support HTML5

GWAMNATIN JAMHURIYAR NIGER TACE SAI TA GANO WADANDA SUKA AIKATA KISSAN SOJOJIN DOMIN DAUKAR FANSA.