Wannan ya nuna cewa an samu Karin miliyan dubu biyu na sefa idan aka kwatanta shi dana shekarar nan.
Karamin ministan dake kula da kasafin kudi Amadu Judud ya bayyana wa majilisar dokokin jamhuriyar Niger cewa kasafin kudin na shekarar badi zaifi mayar da hankali ne akan ayyukan sake farfadowa da kasar ta Niger da ake kira RENASENSIDE.
To sai dai tuni ‘yan majilisar dokoki bangaren adawa suka yi watsi da kasafin kudin.
Sumani Sanda shine shugaban jamiyyar Lumana dake bangaren adawa.
‘’Birjet ya wuce kunga miliyan dubu da dari takwas, amma abinda suka tara shine miliyan dubu dari biyar da hamsin da daya, Kenan kunga ba a tara kudi ba, amma tunda ana son a nuna wa ‘yan kasa kullun aiki akeyi’’….
Ga Yusuf Abdullahi da Karin bayani 2’16
Your browser doesn’t support HTML5