Gwamnatin jahar Kaduna ta kaddamar da shirin ciyar da dalibai ‘yan makarantun firamare a jahar saboda kar wadanda iyayensu matalauta ne su kasa samun irin abincin da zai sa su natsuwa a makarantun.
Da ya ke kaddamar da shirin, gwamna Nasiru El-Rufa’I na jahar ya ce wannan shirin bayar da abinci kyauta ga yara ya fi duk wani shirin da gwamnatin PDP da ta shude ta bullo da shi a jahar. Ya ce bayar da ilimi mai inganci ga yara na da matukar muhimmanci.
Kwamishinan Ilimin jahar Kaduna Dr. Shehu Usman Danfulani, ya ce baya ga taimaka ma yara ‘yan makaranta da iyayensu, wannan shirin zai kuma samar da ayyukan yi ga mata masu dahuwa. Ya ce duk sati kwamnati za ta saki fiye da Naira miliyan 300.
Ga wakilinmu Isah Lawal Ikara da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5