Da safiyar yau Lahadi majalisar ministocin Iraqi ta fidda wani shirin garambawul da za a yi a kasar biyo bayan arangamar da aka yi inda jami’an tsaro suka budewa masu zanga zanga wuta har mutane 19 suka mutu.
Ministocin sun gana a daren jiya Asabar a kokarin da su ke yi na shawo kan zanga zangar da ta ba hukumomin kasar mamaki kwanaki biyar a jere, ta kuma yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 100.
Ministocin sun fidda jerin wasu tsare tsaren garambawul, da zasu duba batun mallakar filaye da gidaje, da daukar sojoji aiki, da karin kudaden tallafin inganta rayuwa ga iyalai marasa karfi, da kuma shirye shiryen da zasu horar da matasa marasa aikin yi.
A wani jawabi da yayi a talabijin a daren jiya Asabar, Firai Ministan Iraqi Abdel Abdul-Mahdi ya fadawa majalisar ministocin cewa a shirye yake ya gana da masu zanga a kasar ya ji korafe korafen su. Ya kuma yi kira ga masu zanga zangar akan su kawo karshen gwagwarmayar da suke yi.