Gwamnatin India Ta Bukaci Kamfanin Facebook Ya Hana WhatsApp Baza Labaran Karya

Mark Zuckerberg, shugaban kamfanin Facebook wanda ya mallaki WhatsApp

Gwamnatin India ta zargi WhatsApp da baza labaran karya wanda ya yi sandiyar mutuwar mutane 31 saboda haka ta bukaci kamfanin Facebook ya hana mutane yin anfani da kafar

India ta bukaci kamfanin Facebook ta hana yada sakwannin karya a kan manhajar WhatsApp, tana mai cewa, wadannan bayanan karya sun sa ‘yan banga sunakashe mutane da dukan mutane a duk fadin kasar.


Sakonin karya game da masu satar yara da ya bazu ta WhatsApp, ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 31 a jihohi goma cikin shekara guda, ciki har da mutane biyar da jama’a suka musu duka har suka kashe su a ranar Lahadi a jihar Maharashtra dake yammacin kasar.


A cikin wata sanarwa da kalamai masu gauni a jiya Talata, ma’aikatar na’urorin da fasahar sadarwa ta India ta fitar, tana cewa, Facebook ba zata iya kaucewa yin bayani da daukar alhaki ba, idan aka yi amfani da wannan manhajar aikewa da sakwannin baza labaran karya.

Sanarwar tace gwamnati ta kuma mika kokenta ga WhatsApp ta dauki matakin gaggawa wurin kawo karshen wannan abu kuma ta tabbatar da ba ayi amfanin da dandalinta wurin baza irin wdannan bayanan karya, inji ma’aikatar fasahar sadarwar India.