Gwamnatin Filato Ta Kaddamar Da Wani Sabon Tsarin Zamantakewa Don Magance Matsalar Tsaro

Gwamnan jihar Filato Samuel Lalong (Facebook/Gwamnatin Filato)

Gwamnatin jihar Filato ta ce ta bullo da wani sabon tsari na fadakar da al’umma kan su sanya ido kan makwabtansu, don gano wadanda ke fakewa suna kashe mutane da yin garkuwa da su.

Sakataren gwamnatin jihar Filato, Farfesa Danladi Atu ya ce sun gano cewa mutane na kwararowa jihar daga wasu wurare suna aikata barna.

Hakan ya sa gwamnan jihar ya umurci jami’an tsaro da su rushe gidan duk wanda aka kama yana boye masu garkuwa da mutane.

Wasu al’ummar jihar sun bayyana cewa suna sa ido kan shiga da fitar jama’a a yankunansu, don haka ma suke bukatar iyaye da su rika yin gargadi wa ‘ya’yansu, gwamnati kuma ta samar da ayyukan yi wa matasa.

Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi a jihar Filato, kuma shugaban karamar hukumar Shendam, Alex Na’antuam ya ce rashin da’a a tsakanin jama’a da ya yi katutu da a baya aka yi biris da shi, shi ne ya kawo ga halin da al’umma ke ciki yanzu, don haka suke daukar matakan hukunci.