Wannan sabon tsarin da gwamnatin shugaba Buhari ta fito dashi yana nuni da cewa ne daraktoci da sauran ma'aikatan gwamnati wadanda suke rike da mukaminsu ba kan siyasa ba zasu cigaba da ayyukansu har sai lokacin da ya kamata su bar aiki, wato mutum ya yi shekaru 35 yana aiki ko ya kai shekaru 60 da haihuwa.
Wannan sabon tsarin ko kuma komawa ga tsarin da aka sani kafin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida wanda ya kawo tsarin da aka soke yanzu, ya jawo cecekuce tsakanin ma'aikatan dake fatan su ma su yi sama idan aka saukar da daraktocin yanzu.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya Alhaji Yayale Ahmed ya yi tsokaci akan wannan matakin na gwamnatin Buhari. Da aka tambayeshi ko wannan tsarin na Buhari zai kawo rudu sai yace ba zai kawo rudu ba.Yace zai ma taimaka ne. A yanayin aikin gwamnati, kwantiragi ne tsakanin gwamnati da wanda aka dauka aiki. Yace a lokacin da aka kawo tsarin saukar da daraktoci mutane sun shiga aiki ne akan zasu yi shekaru 35 suna aiki kafin su bari ko kuma idan sun cika shekaru 60 da haihuwa.
Alhaji Babale yace tsarin ba zai kawo rudani ba domin akwai tanadi a dokar aiki cewa idan wani ma'aikaci baya aikinsa yadda ya kamata akwai hanyar da za'a sallameshi ko a sake mashi gurbi. Yace idan ana bin tsarin aiki a lokacin da mutum ya fara aiki a mataki na takwas kafin ya kai mataki na 17 wanda shi ne matakin darakta ya kusa cika shekaru 35 din. Rashin bin tsarin ne ya sa mutane ke taruwa a sama ana kowa na son zama darakta.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5