Gwamnatin Buhari Ta Na Yiwa Kotuna Da'a

Abubakar Malami ministan shari'a na Najeriya kuma antoni janar

Abubakar Malami ministan ma’aikatar shari’ar Nigeria, yace gwamnatin kasar na bin umurnin alkalan kasar, ba ta sa baki a shari’ar da ake yiwa ‘yan adawa kuma ta na daukan matakan kare lafiyar alkalai da sauran ma’aikatan

Ministan ma’aikatar shari’ar Nigeria wanda kuma shi ne Antoni Janar, Abubakar Malami ya baiyana gwamnatin Shugaba Buhari a matsayin gwamnatin dake yiwa kotunan kasar da’a.

Shari’ah a Nigeria na da fuskoki daban daban. Ta fuskar tsara dokoki, gwamnatin kasar ta gabatarwa majalisar kasar kudurori da dama. Kudurorin na da nasaba da tsaro, cin hanci da rashawa, da ci gaban kasa da makamantansu.

Abubakar Malami y ace an sami karin imani daga ‘yan Nigeria da abun da ya shafi ita kotun. Kafin gwamnatinsu an kai wani lokaci da masu kara za su shiga kotun su yi fito na fito da alkali. Yanzu kuwa ‘yan Nigeria na amincewa da hukuncin kotu kana ita ma gwamnati tana da’a da bin umurnin kotu.

Abubakar Malami y ace a yau an “dauki matakan yiwa soji hukunci da makamantansu da suka yi sama da fadi da dukiyar al’umma” ‘Yan siyasa ma har na jam’iyyar APC ba su tsira ba.

Akan zargin cewa kotu tafi saurin yankewa ‘yan adawa hukumci, Abubakar Malami ya ce wannan ba kyakyawan hukumci ba ne. Gwamnoni biyun da aka yankewa hukumci ‘yan jam’iyyar APC ne.

Dangane da kare lafiyar alakalai da sauran ma’aikata shari’a, Abubakar Malami y ace gwamnati ta kara masu Naira biliyan 10 kan kasafin kudinsu na bana domin inganta tsaronsu da kayan aiki.

A saurai rahoton Baba Yakubu Makeri

Your browser doesn’t support HTML5

Abubakar Malami Ya Ce Gwamnatin Buhari Na Yiwa Kotuna Da'a - 4' 27"