Ministan yace wannan shirin ba wani sabon abu ba ne domin da can an bullo da shirin rage radadi na SUREP ko tun zamanin sojoji gwamnati ta fito dasu sakamakon kara kudin man fetur.
Ministan ya yi bayani kan yadda gwamnati zata rabawa mutane miliyan takwas nera biliyan dari biyar shirin da ya kira matakin farko na taimakawa wadanda suka fi talauci a kasar wajen basu jari da samun dogaro ga kai.
Yace wannan shi ne karon farko da gwamnati don kashin kanta take ware kudin tallafi a cikin kasafin kudin bana domin matakin farko ta dauki wadanda suka kammala karatun digiri dubu dari biyar aiki.
Na biyu gwamnati zata dauki mutane dubu dari masu ilimin fasaha sana'o'i haka nan gwamnati zata dinga samarda abinci sau daya a wuni ga yara 'yan makaranta miliyan biyar da dubu dari biyar.
Ministan ya cigaba da cewa gwamnati zata dinga bada nera dubu biyar wa 'yan Najeriya miliyan daya dake cikin halin kakanikayi kowane wata. Zata ba mutane miliyan daya da dubu dari bakwai da sittin lamuni da suka hada da mata 'yan kasuwa.
Shirin bai tsaya nan ba domin gwamnati zata bada tallafin karo ilimi ga daliban ilimin kimiya da fasaha da lissafi su dubu dari daya.
Alhaji Lai Muhammad yace gwamnati ba zata bari a karkata tallafin ta barauniyar hanya ba.
Gwamnati zata sa kungiyar kwadago a shirin domin a yi adalci kana za'a yi anfani da bayanai daga bankin duniya da asusun Bill Gate domin gano mutanen da suka cancanci samun tallafin.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5