Gwamnatin Brazil Ta Gayyaci jakaden Amurka Ya Yi Bayani

Ma'aikatar NSA

gwamnatin kasar Brazil ta gayyaci jakaden Amurka dangane da wani sabon zargin cewa, shirin hukumar leken asirin Amurka ta na’urori ta sawa shugaba Dilma Rousseff ido.
Jiya Litinin gwamnatin kasar Brazil ta gayyaci jakaden Amurka dangane da wani sabon zargin cewa, shirin hukumar leken asirin Amurka ta na’urori ta sawa shugaba Dilma Rousseff ido.

Jakaden Amurka Thomas Shannon ya gana da ministan harkokin kasashen ketare na Brazil Luiz Alberto Figueiredo, bayan yayata rahoto a tashar talabijin ta Brazil da ake kira Globo cewa, Amurka ta saci karantawa da sauraron sakonnin Ms. Rousseff da shugaban kasar Mexico Entique Pena Nieto.

Jakaden Amurka a Brasilia yaki yin wani bayani dangane da tattaunawarsu.

Yayin wata hira da aka yi da shi ranar lahadi, wani Ba’amurke dan jarida Glenn Greenwald dake yiwa jaridar Guardian aiki, yace ya karbi takardun bayanai daga wurin Edward Snowden wanda ya yiwa cibiyar leken asiri ta NSA tonon silili, da ya nuna cewa, Amurka ta yi satar sadarwar shugabar Brazil da ya hada da sakonnin email da wayoyin tarho.

Greenwald ya kuma shaidawa Globe cewa, takardun da aka rubuta a watan Yuni shekara ta dubu biyu da goma sha biyu sun nuna cewa, an sa ido a sace kan huldar sadarwar shugaban kasar Mexico Enrique Nieto na tsawon wata daya kafin zabenshi.

Ana kyautata zaton Ms. Rousseff zata kawo ziyarar aiki a nan Washington cikin watan Oktoba.