Gwamnatin Borno Ta Fara Maida 'Yan Gudun Hijira Gida

Dr. Babagana Umar Zulum

Gwamnatin jihar Borno ta soma maida mutanen da rikicin boko haram ya dai daita zuwa garuruwansu na asali da gina masu muhallin su sakamakon yan kwarya- kwaryan zaman lafiya da aka soma samu a wasu kyauyuka.

Gwamnatin jihar ta gina sababbin gidaje guda dari biyar a kauyen Ajiri da wasu rukunin gidajen guda tamani a Auno a kananan hukumomin Mapa da Konduga da samar da ruwan sha a wadannan kauyuka da kayayyakin abinci ta kuma bada tallafin Naira dubu hamsin hamsin ga kowane magidanci da aka sake tsugunarwan.

Kwamishinan ma’ikatar gine gine da sake tsugunar da jama’a Injiniya Mustpha Gubiyo, ya ce a yanzu haka akwai mutane sama da dubu biyu da aka riga aka tugunar da su a wadannan kauyuka kuma gwamnatin ta tabbatar da an basu abubuwa da suke bukata na yau da kullum.

Ya ce gwamnatin jihar tana aikin hadin gwiwa da ma’ikatar ministan noma domin raba musu gonaki su fara aiki. Ya kuma bayyana cewa, gwamnati tana aiki da sojoji da “Civilian JTF” da ‘yan sanda da kuma ‘yan banga domin tabbatar da tsaro a kauyukan.

A cikin hira da Sashen Hausa, wadansu mazauna kauyukan sun bayyana matukar jin dadin su da wannan taimako da suka samu daga gwamnati. sun kuma bayyana niyarsu ta ci gaba da gudanar hakokin su na yau da kullum ba tare da tsoron ayyukan ‘yan ta’adda ba, saboda yanzu babu batun Boko Haram.

Saurari rahoton Haruna Dauda Biu cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

AN MAIDA 'YAN GUDUN HIJIRA GIDA