Gwamnatin Borno Ta Bada Naira Miliyan 100 Ga Mutanen Bama

Gwamna Kashim Shettima yana ziyarar kasuwar garin Bama da aka kona kurmus a watan Afrilun 2013. Gwamnatinsa ta ba mkutanen garin agajin Naira miliyan 100

Gwamnatin Kashim Shettima ta ware wannan kudin agajin gaggawa domin tallafawa mutanen da suka yi hasara lokacin da 'yan bindiga suka kai farmaki kan garin.
Gwamnatin Jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ta cire Naira miliyan 100 domin tallafawa wadanda suka yi hasara a lokacin da 'yan bindiga suka kai farmaki, suka yi kaca-kaca da garin Bama dake cikin Jihar a watan Afrilu.

Kimanin mutane dubu daya da dari biyar da hamsin suka rasa gidaje da wuraren kasuwancinsu a garin na Bama, a lokacin da wadannan 'yan bindiga na kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram suka far ma garin a ranar 7 ga watan Afrilu, har aka zub da jini mai yawa.

Tun daga lokacin ne gwamna Kashim Shettima na Jihar ya kafa Kwamiti karkashin jagorancin Alhaji Usman Iidda Shuwa domin binciko irin hasarar da aka yi da wadanda suka yi hasarar da nufin ba su irin taimakon da za a iya.

A bayan da kwamitin ya mika rahotonsa, gwamna Shettima yayi zaman gaggawa da majalisar zartaswarsa, inda suka amince da cire Naira miliyan 100 domin tallafawa mutanen na garin Bama.

Wakilin sashen Hausa, Haruna Dauda Biu, ya aiko da cikakken rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Borno Ta Bada Agajin Naira Miliyan 100 Ga Mutanen Bama - 3:35