Gwamnatin Bauchi Ta Tabbatar Da Cewar Ma’aikatan Lafiya 15 Sun Kamu Da Coronavirus

Kwamitin yaki da cutar COVID-19 a jihar Bauchi ta tabbatar da cewa ma’aikatan lafiya 15 sun kamu da cutar coronavirus a jihar, da suka hada da likitoci da kuma sauran masu aikin jinya.

A kan haka kwamitin ya ce zai shirya ba da horo ga ma’aikatan kula da lafiya kan yadda ake kula da masu cutar COVID-19.

Mataimakin shugaban kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar Bauchi, wanda har ila yau shi ne kwamishinan lafiya na jihar, Dr. Aliyu Muhammed Maigoro ya ce ya zuwa yanzu ma’aikatan lafiyar kadai ne su ka kamu da cutar. "Gwamnatin jihar za ta yi iya kokarinta na ganin ta baiwa ma’aikatan lafiya horo na musamman" in ji shi.

Dr. Aliyu Muhammed Maigoro, ya kara da cewa gwamnatin jihar Bauchi ta na kokarin kafa cibiyoyin gwaje-gwajen cututtuka a duk fadin jihar.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Abdulwahab Muhammad.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Bauchi Ta Tabbatar Da Cewar Ma’aikatan Lafiya 15 Sun Kamu Da Coronavirus