Ofishin jakadanci Amurka na kasar Nijar ne ya damkawa hukumomin kasar talllafin kayayyakin da za'a yi anfani dasu domin yin sintiri akan kogin Isa da na Kwara inda 'yan ta'ada da masu safarar kwayoyi ke ratsawa.
Kwamandan Muhamman Nasiru wanda yake shugabancin jami'an tsaro kan ruwa a yankin Yamai yace horan ya dauki sati biyu. An koya ma sojojin anfani da jiragen ruwa da yadda ake gyaran jiragen.
Shi kogin Isa ya hada Nijar da Mali da Najeriya yankin dake fama da yaki da ta'addanci. Saboda haka horon zai taimaka wurin yaki fa ta'addanci a kan ruwa.
Tallafin wani bangare ne na zunzurutun kudaden da Amurka ke kashewa kasar Nijar a fannin yaki da ta'addanci kamar yadda Alhaji Idi Barau, jami'in hulda da jama'a a ofishin jakadancin Amurka a Nijar ya bayyana..
Alhaji Barau ya fayyace kudaden tallafin. Yana mai cewa kayayyakin da Amurka ta baiwa Nijar sun kai dalar Amurka dubu dari biyar. A shekarar 2016 Amurka ma ta kashe dalar Amurkan miliyan goma sha shida domin tallafawa hukumomin Nijar a yaki da ta'addanci.
Kwamandan rundunar tsaro a yankin na Yamai ya yabawa wannan yunkurin na Amurka tare da cewa tallafin zai yi tasiri sosai wajen cin nasarar ayyukan da aka sa gaba.
Ga karin bayani daga rahoton Souley Barma.
Your browser doesn’t support HTML5