Gwamnatin Amurka Na Binciken Kafa Sada Zumuntan Masu Son Shigowa Amurka

Obama

Gwamnatinn Amurka ta fara tamnbayar baki daga kasashen waje da suke ziyara a kasar su bayyana kafar sada zumunta da suke amfani da ita, a zaman wani yunkuri na gano wadanda zasu iya zama 'yan ta'adda.
Tun a makon jiya, 'yan kasashen waje wadanda suke ziyara a kasar karkashin shirin na daga kasashen da'a bukatar visa domin zuwa Amurka, ana tambayarsu su bayyana suna da kuma adireshin kafofin sda zumunta da suke amfani da su.
Kodashike ba tilas bane, kuma jami'ai suka ce ba zasu hana mutum shiga Amurka wanda yaki bada wadannan bayanai ba, matakin ya janyo suka daga wasu cibiyoyin Amurka dake kare 'yancin walwala da demokuradiyya da kuma, kamfanonin fasaha.
Haka nan masu sukar lamirin shirin, suka ce ana iya amfani da shi wajen auna larabawa da msuulmi wanda zai sa a rika musu bincike sosai.
Wata tawaga da take wakiltar kamfanoni da suka hada d a Facebook, da Twitter,da Google, kungiyar kamfanonin masu samarda internet, duk sun dake cewa matakin ya sabawa 'yancin magana.