Gwamnatin Aljeriya Ta Tasa Keyar 'Yan Nijar 644 Zuwa Kasarsu

Ministan Harkokin Wajen Nijar Mohamed Bazoum

Kamar yadda ta saba yi gwamnatin Aljeriya ta tasa keyar wasu 'yan kasashen yammacin Afirka zuwa Nijar kodayake yawancinsu da suka kai 644 'yan Nijar ne amma ministan harkokin cikin gida ya ce Aljeriya na iya tura sauran zuwa kasashe goman.

Algeriya ta tusa keyar wasu 'yan asalin kasashen yammacin Afirka 11 da suka hada da 'yan Nijar 644.

Aljeriya ta saba dawo da 'yan asalin Afirka ta jibgesu a Nijar tare da zargin su da shiga kasarsta ba kan ka'ida ba.

Matasan Nijar da aka taso keyarsu na cewa, zuwan su Aljeriya ba domin jin dadi ba ne, matsala ce ta haddasa barin kasarsu amma idan gwamnati ta taimaka masu da abun yi, babu dalilin da zata sa fita zuwa wata kasa kuma.

Rashin aiki da rashin kulawa daga hukumomin kasashen su suka sasu fita kodayake sau tari hukumomin Nijar na cewa suna iyakar kokarin su na taimakawa. Gwamnatin Nijar ta yi watsi da zargin da matasan keyi.

Malam Usman Musa dan kwamitin dake karbar 'yan Nijar da aka koro daga kasar Aljeriya, ya ce suna aiki haikan domin tabbatar cewa wadanda aka koron sun isa garuruwansu lafiya.

Bazoum Muhammad, Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Nijar ya ce gwamnatin kasar tana shirye ta yiwa 'ya'yanta marhaban a duk lokacin da aka dawo dasu daga wata kasa. Sai dai ya nuna bacin ransa game da jibge 'yayan wasu kasashen a Nijar da Aljeriya ta yi.

Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Aljeriya Ta Tasa Keyar 'Yan Nijar 644 Zuwa Kasarsu - 3' 49"