Jami’an tsaron kasar Afghanistan masu fafatawa da kungiyar Taliban sun yi asaran mayakansu har dubu 15 da suka mutu, ciki ko har da sama da dubu 5 da aka hallaka a cikin wattani 8 na farkon wannan shekarar, kamar yadda wata hukumar nazari ta Amurka ke bayyanawa.
A cikin rahotonsa na watani ukku-ukku da yake bayarwa da aka wallafa jiya Lahadi, Babban Sufetan Hukumar sake Tada Komadar Afghanistan, yace gwamnatin kasar ta yi hasarar akalla kashi biyu da digo biyu na yankin kasar lokacin da ake wannan fada da kungiyar ta Taliban a cikin wannan shekara.
Jami’in ya bada misali da cewa daga cikin gundumomi fiyeda 250 dake karkashin rikon gwamnatin Afghanistan, mayakan na Taliban sun kwace 33 a cikin wannan shekarar.
Kungiyar ta Taliban dai ta kara kaimi a bakin daga da sauran wasu wuraren da take kai hari daga watan Agusta zuwa yanzu, wanda haka yasa tayi kusa ta kame birnin Kunduz dake arewancin kasar da kuma shelkwatar lardin Helman duka a cikin wannan watan.