A dai dai lokacin da hankula ke kwantawa biyo bayan tashe tashen hankula da rikicin kabilancin da suka auku cikin kwanakin nan a wasu sassan jihar Adamawan, yanzu haka gwamnatin jihar ta umarci shugabanin da kuma masu fada aji,da su tashi tsaye wajen fadakar da al’umma muhammancin zaman lafiya.
A wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar, Gwamnan jihar Senata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla yace dole yan jihar su yi karatun ta natsu ganin illar dake akwai a tashe tashen hankulan da suka auku cikin kwanakin nan,musamman a yankunan Numan da Demsa,wanda ke da nasaba da fadan kabilanci.
Gwamnan ta bakin hadiminsa ta fuskar harkokin yada labarai, Mr Martins Dickson yace gwamnati ba za ta kyale wasu dake daukar doka a hannunsu ba, yayin da ya yaba da kokarin da wasu suka soma na kawo fahimtar juna a cikin al’umma.
Yayin da gwamnatin jihar ke wannan kira, ga mutane irinsu AlhajiYayaji Gombi wani dan siyasa a jihar na ganin dole su ma shuwagabanin addini su shigo a wannan yunkuri na kawo fahimtar junan.
Ita kuwa a nata bangaren kungiyar hadin kan yan Adamawa, ta Adamawa United Forum, kokawa ta yi da rashin hukunta masu laifi a tashe tashen hankula, da zama dalilan wadannan matsaloli na rikicin makiyaya da manoma a jihar. Musa Jekeko dake zama shugaban kungiyar a wani taron manema labarai ya bayyana hakn.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, bayanai na cewa akwai wasu gungun matasa da ba jami’an tsaro ba,da suka kafa shinge a hanyar Lamurde har zuwa garin Tigno suna cajan masu shiga ko wucewa wadanda ba yan kabilar yankin ba ne. Batun yana bukatar bincike.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5