Gwamnatin Adamawa Ta Mayarwa NYSC Sansanin Horas da Masu Yiwa Kasa Hidima

Bikin mayar da sansanin da mataimakin gwamnan jihar ya kaddamar

Gwamnatin jihar Adamawa ta mikawa hukumar kula da masu yiwa kasa hidima, NYSC, sansanita na dindindin dake Damare a karamar hukumar Girei bayan shekara hudu tana anfani da shi don tsugunar da ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya daidaita.

Mataimakin gwamnan jihar Adamwa Injiniya Martin Nasir Babale ya fadawa wakilin sashin Hausa bayan ya mika makullan ga shugaban hukumar cewa sun maida wa hukumar sansanin sakaamakon kwanciyar hankula da aka soma samu a yankuna da rikicin Boko Haram ya shafa wanda ya yi dalilin raguwar adadin ‘yan gudun hijiran daga sama da dubu shida zuwa kasa da dubu biyu.

A baya dai masu yiwa kasa hidima da ake aikawa jihar Adamawa na karbar horo a jihohin Binuwai, Naija, Kogi, Kano da Gombe ne saboda rashin tabbas na tsaro a jiha da tayi fama da tashe-tashen hankula na ta’addanci inji shugaban hukumar kula da masu yi wa kasa hidima na jihar Adamawa, NYSC, Mal. Mohammed Abubakar.

Sansanin horas da NYSC na din din din dake Damare

Ya ce sake bude sansanin na zuwa biyo bayan tabbacin da hukumar ta samu daga ofishin mai baiwa shugaban kasar Najeriya shawara kan harkokin tsaro, amma ya ce har yanzu hukumar ba ta tsaida shawarar aikewa da masu yiwa kasa hidima kananan hukumomin Madagali da Michika ba, wuraren da har yanzu ke fama da hare-haren Boko Haram jifa-jifa.

Kwamishinan filaye da safiyo na jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin sake gyara sansanin Alhaji Yayaji Mijinyawa ya ce kawo yanzu kwamitin ya kashe sama da naira miliyan bakwai wajen maida kayayyakin da aka lalata.

Tuni har wasu masu yiwa kasa hidima sun soma isa sansanin don a yi masu rajista, Wani mai yi wa kasa hidima daga jihar Imo Mr, Ogwoma Chinedu ya shaidawa Muryar Amurka saduwarsa da shugaban hukumar wanda yace ya dau alkawarin samar masu da ruwa ya kuma cika.

Saurari Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnatin Adamawa Ta Mayarwa NYSC Sansanin Horas da Masu Yiwa Kasa Hidima - 2' 54"