Gwamnati Zata Janye Fasfo Na Diflomasiya daga Wadanda Basu Cancanta Ba

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Biyo bayan umurnin da shugaba Buhari ya bayar na janye fasfo din diflomasiya daga wadanda basu cancanta ba, hukumar shige da fice tace bin umurnin ya zama dole

A farkon wannan makon ne shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bada umurnin a janye fasfon na diflomasiya da na hukuma daga hannun mutanen da doka bata amince masu ba.

Kakakin hukumar shige da fice wato immigration service a turance kuma mukaddashin kwanturola yace idan shugaban kasa ya bada umurni to dole alatilas a bi umurnin.

Kamar yadda kakakin ya yi bayani a hukumance shugaban kasa da mataimakinsa da kakakin majalisar dattawa da mataimakinsa da tsoffin shugabannin kasa da jakadu da ministoci da gwamnoni masu ci ya kamata su rike fasfo na diflomasiya. Tsoffin gwamnoni ko ministoci basu cancanta su rike fasfo na diflomasiya ba. Wadanda kuma zasu iya rike fasfo na diflomasiya sai wadanda ma'aikatar harkokin waje ta amince masu.

Tsohon ministan harkokin wajen Najeriya Dr. Aliyu Idi Hong yace dama fasfo na diflomasiya kayan gwamnati ne. Jakada ko wanda zai wakilci gwamnati a waje a ke baiwa domin samun taimako wurin neman biza wato takardar izinin shiga wata kasa. Amma da zara mutum ya bar aikin gwamnati yadda zai bar ofishin gwamnati da gidan gwamnati haka ya kamata ya bar fasfo na diflomasiya.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnati Zata Janye Fasfo Na Diflomasiya daga Wadanda Basu Cancanta Ba