A bara cikin watan bakwai, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya baiwa jami'an gwamnati umarnin su tattauna da 'yan kungiyar Boko Haram, a yunkurin gwamnati na cika alkwarin data yi na ganin an sako 'yan matan- su metan da 'yan kai, da 'yan binidgar suke ci gaba da karkuwa da su.
Ministan yada labarai da kula da al'adun garjiya da yawon bude ido, Alhaji Lai Mohammed, ne, ya bayyana haka a wani taro da yayi da manema labarai, a karshen makon jiya.
Lai yace, ana daf da kammala shawarwari, sai 'yan binidgar suka sake shawara suka gindaya wasu sabbin sharudda, wadanda gwamnati bata gamsu da su ba.
Da aka tuntubeta kan wannan ikirari na gwamnati, daya daga cikin wadanda suke fafutukar ganin an saki 'yan matan, Aisha Yusuf, ta gayawa Madina Dauda cewa, zasu binciki wannan magana domin tabbatarda sahihancinta.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5