An bukaci Kwamitin wanda ya kunshi kwarraru a bangarori daban-daban a cikin gwamnatin kasar da kungiyoyin cigaba na kasa-da-kasa masu zaman kan su domin samar da ingantattun shawarwari da za su lalubo mafita ga matsalar.
Ministan Shari'a na kasar Abubakar Malami ne ya kaddamar da kwamitin ya kuma bayyana makasudin gwamnatin kasar na kafa shi, tare da zimmar baiwa gwamnati shawarwari da suka dace a kan matakin da ya kamata a dauka.
Malamim makarantar kimiya da fasaha ta Jihar Kaduna Abdulhakeem Garba ya yaba da wannan mataki na gwamnati inda ya ce hakan zai rage yawan cin zarafi da ake yi wa mata a kasar.
"Lalle abu ne wanda ya kamata ya faru tun tuni, zai iya taimakawa, amma fa a tuna cewa wasu matan su suke kokarin tunkarar maza da magaña soyayya, sai daga baya su yi musu kazafi."
Sai dai a nata bangaren, Haiya Amina Bibi Farouk da ke rajin kwato wa mata hakokkinsu ta ce "an dade ana ruwa kasa na shanyewa, hanya daya tilo da ya kamata a cigaba da bi shine wayar da kan al’umma game da fyade da nau’ukan cin zarafi."
"Babbar abinda ke janyo wannan fyaden shi ne rufa-rufa, ya kamata a dinga yi wa mutane shari'a kan laifukan cin zarafin da suke aikatawa."
Wannan kwamiti dai ana sa ran zai samar da hanyoyi mafi dacewa wajen tunkarar lamarin da ke neman zama ruwan dare a kasar.
A cewar kungiyoyin kare hakkin bil adama a cikin kwanakin nan kullum sai sun samu mutane da dama da aka ci zarafinsu a Najeriya.