Daukacin shugabannin sojojin Najeriya kama daga sojojin kasa zuwa na ruwa da na sama duk suna jihar Rivers domin ganin yadda zasu hada karfi da karfe su kawo karshen tashin tashinar tsagerun Niger Delta.
Jiya shugabannin sojojin da gwamnan jihar Rivers da shugabannin kamfanin da tsagerun Niger Delta suka fasa bututunsu suka yi taro inda suka cimma matsaya daya akan tsagerun.
Baicin haka sojoji sun kaddamar da sabbin jiragen ruwan yaki goma sha biyu domin fuskantar 'yan tsagerun.
Mai magana da yawun sojin Najeriya Kanar Kukasheka yace akwai matakai da dama da suke dauka tare da wasu karin da ake niyyar dauka kan tsagerun. Yace tsagerun basu da wani koke, kawai dai barayi ne. Sata da kwace suka sa a gaba tare da neman yiwa kasa zagon kasa.
An jawa tsagerun kunne su daina aika-aikarsu domin babu yadda gwamnati zata amince da irin barnar da su keyi. Suna farma jama'a ba gaira ba dalili. Suna farma wasu kaddarori na kasa lamarin dake kara dagula tattalin arzikin kasar. Banda haka hatta sojoji suke farma su kashesu.
Dangane da cewa sai an hada da lalama za'a iya shawo kan tsagerun kamar yadda Edwin Clark ya bukaci gwamnati tayi, Kanar Kukasheka yace wannan ra'ayinsa ne. Yace babu yadda za'a yi a bar wasu suna lalata abun da tattalin arzikin kasar ya ta'allaka a kai. Misali rabon arzikin kasa da a keyi wata wata jihar Rivers da nera biliyan goma sha bakwai take samu amma yau an wayi gari biliyan uku kacal ta samu sanadiyar fasa bututun mai.
Ga cikakken bayani.
Your browser doesn’t support HTML5