Gwamnatin jihar Kano ta bullo da wani shirin na wayar da kan matasa ta hanyar jan su a jiki da nuna musu ilolin shan miyagun kwayoyi tare da nuna musu muhimmanci dogaro da kai da mayar dasu muhimman mutane a cikin al’uma.
Mai taimakawa Gwamnan jihar Kano, kan harkokin matasa Hajiya Surayya Aminu, ce ta furta haka a lokacin da suka yi wata tattaunawa da wakiliyar Dandalinvoa, Baraka Bashir, a birnin Kano.
Hajia Surayya ta ce lokaci yayi da matasa za su san cewar shan miyagun kwayoyi bashi da wani amfani illar salwantar da rayuwarsu tare da mai da su koma baya a acikin al'uma.
Ta kara da cewa gwamnati zata taimakawa masu bukatar ilimin naurar kwamfuta kyauta da kuma koyon sanao’i daban daban.
Ta ce tuni suka fito da wasu hanyoyin inganta matasa ta hanyar horar da su tare da basu jari domin dogaro da kai, inda suke bayyan illolin tare da hadarin rashin ilimi.
Your browser doesn’t support HTML5