Gwamnati Ta Bayyana Shirinta Na Gina Cibiyoyin Kimiyya Da Fasaha A Jami'o'in Najeriya

Gwamnatin tarayyara Najeriya ta bayyana shirinta na gina cibiyoyin kimiyya da fasaha a jami’oin kasar a yunkurin ta na inganta harkokin kimiyya da fasaha a daukacin kasar.

Jawabin shugaba Muhammdu Buhari, ne ya bayyana haka jiya litini a birnin tarayya Abuja, yayin da yake jawabi a babban taron kimiyya da fasaha na kasa wanda aka yiwa lakabi da bind Kadin kimiyya da fasaha a najeriya domin cigaba mai dorewa a bangaren kimiyya da da fasaha.

Shugaban da mataimakin shugaban kasa Yomi Osinbajo ya wakilta ya bayyana cewa gina cibiyoyin kimiyya da fasaha a jami’oin kasar wata dama ce ta habaka kirkire-kirkire da fasaha a zukatan matasa domin samar da cigaba a harkokin kimiyya da fasaha.

Ya kuma kara da cewa manufar gwamnatin Najeriya ita ce ta yi amfani da wadannan dabaru wajan cusawa matasa ra’ayin gina kai a fannin kimiyya da fasaha da kuma gogaiya da sauran kasashen duniya a fagen kimiyya da fasaha.

A watan satumba na shekarar 2016, ne majalisar tarayyar Najriya ta amshi bakuncin baje hajar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha daga sassa daban daban na kasar, daga wannan lokaci ne babban bankin duniya ya cigaba da bada goyon bayan wannan yunkuri ta hanyar bada tallafin kudi dalar Amurka miliyan 3, wanda aka riga aka tsin-tsinka domin ci gaba da habaka wannan yunkuri.

Ya kara da cewa “ina mai farin cikin bayyana maku cewa babban bankin duniya ya bada tallafin kudi dalar Amurka miliyan uku domin tallafawa shirin a dukkan jami’oin dake fadain kasar.i,

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ne ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari wajan bayyana sakon a jiya litini a birnin tarayya Abuja, yayin da yake jawabi a babban taron kimiyya da fasaha na kasa wanda aka yiwa lakabi da bind Kadin kimiyya da fasaha a najeriya domin cigaba mai dorewa a bangaren kimiyya da da fasaha.

Shugaban da mataimakin shugaban kasa Yomi Osinbajo ya wakilta ya bayyana cewa gina cibiyoyin kimiyya da fasaha a jami’oin kasar wata dama ce ta habaka kirkire-kirkire da fasaha a zukatan matasa domin samar da cigaba a harkokin kimiyya da fasaha.

Ya kuma kara da cewa manufar gwamnatin Najeriya ita ce ta yi amfani da wadannan dabaru wajan cusawa matasa ra’ayin gina kai a fannin kimiyya da fasaha da kuma gogaiya da sauran kasashen duniya a fagen kimiyya da fasaha.

A watan satumba na shekarar 2016, ne majalisar tarayyar Najriya ta amshi bakuncin baje hajar kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha daga sassa daban daban na kasar, daga wannan lokaci ne babban bankin duniya ya cigaba da bada goyon bayan wannan yunkuri ta hanyar bada tallafin kudi dalar Amurka miliyan 3, wanda aka riga aka tsin-tsinka domin ci gaba da habaka wannan yunkuri.

Ya kara da cewa “ina mai farin cikin bayyana maku cewa babban bankin duniya ya bada tallafin kudi dalar Amurka miliyan uku domin tallafawa shirin a dukkan jami’oin dake fadain kasar.

Your browser doesn’t support HTML5