Gwamnatoci, daga kananan hukumomi, zuwa na taraiya na kokari domin ganin cewa mutane basu kamu da cutar Ebola ba.
WASHINGTON, DC —
Tun lokacin bullar cutar Ebola, kawo yanzu gwamnatoci, daga kananan hukumomi, zuwa na gwamnatin taraiya ke iya bakin kokarinsu domin ganin cewa mutane basu kamu da wannan cutar ba.
Domin su kansu likitocin, sun ce cikin kashi goma, da kyar ake samun kashi, hudu da zasu tashi idan wannan cutar ya kama su.
Ba mamaki wannan yasa gwamnatocin ke yin duk abunda ya dace domin ganin cewa jama’a basu kusanci samu wannan cutar ba.
Daya daga hanyoyin da ake kamuwa da wannan cutar kuwa ya hada da cin naman daji, da suka hada da Gada, Goggon biri, da Biri, wannan yasa Gwamnati ta bada umari cewa a dan kauracewa wadannan dabbobin tukunna har na wani lokaci.
Your browser doesn’t support HTML5