Allurar rigakafi ce na cutar zazzabin cizon sauro ga yara masu shekaru watanni biyar zuwa watanni 36 kuma dole ne a adana allurar a yanayin zafi tsakanin digiri biyu zuwa takwas.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa, matsakaicin alkaluma na nuni da adadin sama da mutane 600,000 ne ke mutuwa a sanadiyyar zazzabin cizon sauro a kowace shekara, yayin da yaro daya ke mutuwa a duk minti daya.
Yara a Afirka ne suka fi fuskantar hadarin mutuwa daga wannan cuta. Sai dai kuma, masana kimiyya a jami'ar Oxford da ke Birtaniya sun ce sun shafe shekaru da dama suna bincike kan rigakafin.
Wannan ci gaban ya kawo sauyi a fagen yaki da zazzabin cizon sauro, wanda ke daya daga cikin manyan cutar dake kashe-kashen yara a Afirka.
An ce maganin yana da tasiri kashi 80% kuma Cibiyar Serum ta Indiya ta kera shi. Ghana ce kasa ta farko a nahiyar Afrika da ta amince da fara amfini da rigakafin.
Hukumar Lafiya ta Duniya tana nazarin ko za ta amince da maganin, kuma ana shirin samar da allurai miliyan 200 a duk shekara.