Gwamnati Na Daukan Matakan Kare Masu Fallasa Almundahana - Malami

Abubakar Malami ministan shari'a na Najeriya kuma antoni janar

A firarsa da Muryar Amurka Abubakar Malami ministan shari'a na Najeriya yace kwalliya ta fara biyan kudin sabulu domin kowace rana ta Allah ana samun kudade suna shiga aljihun gwamnati sanadiyar ba mutane dama su fallasa duk wani almundahana tare da bada tukwuici

'Yan kasar da dama suna kai komo ofishin hukumomin kasar da suka hada da na antoni janar da ma'aikatar kudi da EFCC da ICPC suna bada bayanai na gaggawa.

Bayanan da jama'a ke bayarwa a asirce ba kawai kan almundahana da kudi suka tsaya ba. Akwai bayanan hanyar da mutane suke samun makamai suna boyesu.

Akan makoman mutanen da suka tafka sata. Ministan yace suna daukan matakai biyu. Mataki na daya shine kudin da "aka yi sama da fadi dashi ya dawo aljihun gwamnati", inji Abubakar Malami. Mataki na biyu shi ne duk wanda zargin sata ya tabbata a kansa na cewa yayi sama da fadi a bi mataki na ukuba gareshi, a cewar Abubakar Malami.

Dangane da makomar mutanen dake fallasa almundahana sai Ministan Shari'a, Abubakar Malami yace gaskiya ne akwai koke na cewa an dauki matakin korar wani daga aikinsa saboda ya tseguntawa gwamnati wata sata da aka yi. Yace an kafa kwamiti na koli a fadar mataimakin shugaban kasa dangane da matsalolin da masu fallasa ka iya fuskanta.

Ta fuskar kariya ana daukan matakan kare masu tseguntawa gwamnati ayyukan almundahana da suka hada da yin bincike da muamala ta aikin gwamnati tare da tabbatar da cewa an yi masa adalci.

Dangane da ire-iren kudaden da ake kwatowaAbubakar Malami ya bayyana irin rawar da ma'aikatar shari'a zata taka saboda yin anfani da kudaden ta hanyoyin da suka dace. Yace za'a bi dokokin kasa da shari'a ta tanada.

Ga firar da Muryar Amurka tayi

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnati Na Daukan Matakan Kare Masu Fallasa Almundahana - Malami - 4' 32"