Wasu malaman makarantun Firamare a jahar Adamawa sun gudanar da zanga-zanga ta lumana zuwa gidan gwamnatin jahar dake Dogire, domin nuna damuwarsu kan rashin biyansu albashi.
Duk da cewa sakataren gwamnatin jahar da kuma kwamishinan kananan hukumomi sun tarbesu, abunda ya biyo baya yanzu yasa wasu malaman suna buya.
Rahotanni da muka samu sun nuna cewa 'Yansanda suna bi makaranta makaranta suna kama malamanda suka shiga jerin gwanon. Wadansu daga cikin malaman wadanda basu amince wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz, ya dauki muriyarsu ba, sunce jami'an tsaro suna bi daya bayan daya ana kama su.
Amma shugaban kungiyar malaman (NUT) Komored Dauda Maina, wanda har wayau shine shugaban kungiyar kwadago ta kasa reshen jahar watau (NLC), ya nesanta kungiyar daga matsalar da malaman suka shiga.
Amma da yake nesanta gwamnatin jahar kan kame-kamen da ake yiwa malaman,kwamishinan yada labarai na jahar Mal Ahmed Sajoh, yace wani daga cikin malaman da suka shiga jerin gwanaon, ya gayawa bangaren gwamnati cewa, kungiyarsu ta malaman ce tasa ake kama su.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5